Sharhin Littafin Arabaeenan Nawawi - Gabatarwa
SHARHIN
LITTAFIN
HADISIN
ARBA’EENAN-NAWAWI
(شرح الكتاب الأربعين النووية)
Na
Nana A’isha Muhammad
GABATARWA
Godiya ta
tabbata ga Allah (S.W.T.), Mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su
kara tabbata ga Annabinmu Habibinmu Abin koyinmu Muhammad (Salaawatullahi
alayhi) da alayensa da sahabbansa adalai da wadanda suke koyi da bin
tafarkinsa har izuwa ranar sakamako.
Hakika Allah
Madukakin Sarki Yana cewa a cikin Alkur’ani, Suratul Juma’a aya ta 2:
هُوَ ٱلَّذِى بَعَثَ فِى ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ
رَسُولاً مِّنۡہُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡہِمۡ ءَايَـٰتِهِۦ وَيُزَكِّيہِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ
ٱلۡكِتَـٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ
“Shi
ne (Allah) Wanda Ya aika, a cikin mabiya al’adu (marasa rubutu da karatu), wani
Manzo daga gare su yana karanta ayoyinSa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma
yana sanar dasu Littafin da hikima ko da yake sun kasance daga gabaninsa lallai
suna a cikin bata bayyananne”.
Bayan saukar da
Alkur’ani da Allah Yayi ga zababben wannan al’ummar (wato Annabi Muhammad S.A.W.)
[e.g. Musnad Ahmad: 13,909]. Sai kuma Allah Ya bashi iko da dama
da zai yiwa al’ummar bayanin dukkan abin da ya shafi addini da rayuwa wahyan
da hikiman (Hikima itace ‘Sunnah’ in ji Imam
Ash-Shafi’i) [Qur’an: Saf: 9], ta hanyoyi da suka hada da ya aikata (فعل) sai kwaikwayeshi, ko ya bada umarni (أمر) sai a bi, ko ya hana (نهي) sai a hanu, ko a yi a gabansa bai yi
magana تقرير (bai ce a daina aikatawa ba), to ruwaito wadannan abubuwan shi ake
cewa Hadisi a wajen malaman hadisi a takaice.
Hadisi kuwa, indai
ya tabbata ingantacce daga Manzon Allah (S.A.W.) ba mu da kokwato cikinsa cewa
tabbatas Allahne Ya kunsawa Annabi (S.A.W.) domin ya isarwa mutane da wani sako
saboda shi Annabi (S.A.W.) baya fadin son ransa face wani wahayi da aka masa,
kuma an sanya mana shi (Annabi) ya zame mana abin koyi [Nisa’i: 59; Nahl:
44; Ahzab: 21;Najm, aya ta 3-4].
Za mu fahimci
cewa; Hadisi a wajen Musulmai shi ne madogara ta biyu bayan Alkur’ani da ake
duba izuwa gareta domin kara fahimta ko warware wata mas’ala a cikin addini ko
wani bangare na rayuwa, ko neman karin bayani akan abin da bai fito karara a
Alkur’ani Maigirma baو duba
izuwa ga matn (abin da hadisin ya kunsa) da kuma sanadi (silsilar
yadda aka sami hadisin).
Ilimin sanin hadisi
kuwa fagene mai fadi da malamai suka yi bayaninsa dalla-dalla wanda ya
kunshi bangaro kamar haka: Usulul Hadis, Mustalahul Hadis, ‘Ilm riwaya
wad-dirayatl Hadis, al-Jarh wa’l-ta’dil,’ilm rijal (‘ilm tarikhul riuwat, ma’rifat
awtan al-ruwat wal biladihim, ma’rifat al-mu’talif wal-mukhtalif minal asma
wa-ansab) da sauransu. Daga nan zaka ji an
bawa hadisi wani suna Mutawatir, Ahad, Gharib, ‘Aziz, Mashhur (ta
bangaren adadin wadanda suka ruwaici hadisi). Ko kuma Mudallas, Musalsal
(ta yanayin da aka ruwaito hadisin). Ko kuma Shadh/Shazzi, Munkar, Mudraj
(ta yanayin Matn da Isnadin hadisi). Ko kuma Mudtarib,
Maqlub, Ma’lul/Mu’allal (ta yanayin boyuwar wani abu cikin matn ko
isnad). Ko kuma Sahih, Hasan, Da’if, Maudu’ (ta yanayin rawi,
al-thiqat dss).
Daga cikin Dukkan
wadannan ilmai ba za su koyo ba a kankanin lokaci ko social media
ba, dole sai mutum ya koma wajen malamai yardaddu masana ilimin sosai yana
bibiyarsu tukun mutum zai kamtafa daga koramunsu, Allah Ya sa mu dace.
Wannan dan
takaitacce rubutune akan Sharhi littafin Hadisai na Imam an-Nawawi
wato Arba’una ko Arba’eena Hadisi, ko Arba’eenan
Nawawi cikin harshen Hausa tare da takaitaccen nazari da alakanta hadisan cikin ibada, aqeeda,
mu’alama da sauran bangarorin addini da kuma rayuwa. Ina rokon Allah Ya dafa
min na rubuta daidai, Ya kuma tsare ni da rubuta kuskure ko son zuciya wajen
bayani, Ya sakawa iyaye da kuma malamaina da alkhairi, amin.
Nana A’isha
Muhammad
30th Muharram,
1439AH
21st October,
2017CE
Comments
Post a Comment