Tarihin Sahabbai Mata 1: Maimunatu bint al-Harith (R)
MAIMUNATU BINT
AL-HARITH
(ميمونة بنت الحارث)
" Ita ce
mata ta karshe a gidan Manzon Allah ﷺ "
-
.
Sunanta Maimuna (ميمونة) bint al-Haris (الحارث) bn Hazn (الهزم) Al-Hilaliyya (الهلالية), sunan mahaifiyarta Hind bint Awf (هند بن عوف) ‘yar qabilar Himyar ta
Yemen. Maimunatu bint al-Harith ta kasance 'yar uwar Ummu Fadal (أم فضل). An haifeta a kafin Hijira da shekara 28 a garin.
- Al-Isaba
8/192
Asalin sunanta Barratu (برّة) sai Manzon ﷺ Allah Ya canza mata suna zuwa Maimuna (ميمونة) ma’ana ‘Mai albarka'. Kafin ta auri Manzon Allah ﷺ ta auri Mas'ud bn Amr Athaqafy (مسعود بن عمور الثقفى) tun a lokacin Jahiliya (kafin zuwan Musulunci) sai suka rabu.
Bayan nan sai ta auri Abu Ruhum bn Abdul Uzza (أبو رهم بن عبدالعزى) shi kuma rasuwa (mutuwa) yayi. Bayan rasuwarsa ne sai ta auri Manzon Allah ﷺ a lokacin da akayi Umarar Ramuwa (عمرة القضاء) a watan Dhul-Qa'adah shekara ta bakwai (7) bayan hijira a
Sarif wanda yake da tazarar mil goma (10) tsakaninsa da garin Makkah, a lokacin
tana ‘yar shekara 58 a duniya.
Muhammad bn Umar yace ita ce ta bayar da kanta ga (ta nemi auran)
Manzon Allah ﷺ sai Ya aureta a hannun
baffansa Abbas akan sadaki dirhami dari biyar (500) kamar yadda Ibn Sa'ad (ابن سعد) ya fitar daga Abdullah bin Abbas Yace "Manzon Allah Yace
'yan uwa guda hudu (4) muminaine; Maimuna da Ummu Fadal أم الفضل لبابة الكبرى الهلالية (mahaifiyar Abdullah bn Abbas) da Asma'u bint Umays أسماء
بنت عميس(matar Abubakar R.) da Salma bint Umays سلمى بنت عميس (matar Hamza ibn Abud
al-Muttalib Asadullah).
Kasancewarta matar Manzon Allah ﷺ Ya sanya ta zama malama dake ruwaitu hadisai daga Manzon Allah ﷺ Imamuzzahabi yace "an ruwaitu hadisai goma sha uku 13 daga
gareta.
- Siyaru 2/240; Tarikul Rasul wal-Muluk, 201
Ibn Sa’ad yace tarasu daga wakidiy yace ta rasu tana da shekaru 80 ko 81 a
shekara ta 51 bayan Hijirar Annabi ﷺ daga Makkah zuwa Madinah
zamanin Mulki Yazid dan Mu’awiyyah. Kuma itace karshen rasuwa cikin
matan Manzon Allah ﷺ.
Amma Imamuz-Zahabi yace bata kai wannan lokacin ba lallai ta rasu
kafin Aisha, yace ita ce ta rasu a shekara ta 51 bayan Hijira, bayan ta dawo
daga aikin Hajji, kuma dan ‘yan uwarta (أم الفضل لبابة الكبرى الهلالية) Abdullahi bin Abbas (R) Ya sallace ta Allah. Ya kara mata
yarda.
- Al’isaba 8/192, Siyaru ‘alamin Nubala 2/239-245, Alhakim:
Mustadark 4/32
To be continued… in sha Allah
✍
Mal. Ka'ab Saleh
21st Muharram, 1439AH
12th October, 2017CE
Comments
Post a Comment