Sharhin Littafin Arabaeenan Nawawi - Gabatarwa
SHARHIN LITTAFIN HADISIN ARBA’EENAN-NAWAWI ( شرح الكتاب الأربعين النووية ) Na Nana A’isha Muhammad GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T.), Mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Habibinmu Abin koyinmu Muhammad ( Salaawatullahi alayhi) da alayensa da sahabbansa adalai da wadanda suke koyi da bin tafarkinsa har izuwa ranar sakamako. Hakika Allah Madukakin Sarki Yana cewa a cikin Alkur’ani, Suratul Juma’a aya ta 2: هُوَ ٱلَّذِى بَعَثَ فِى ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ رَسُولاً مِّنۡہُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡہِمۡ ءَايَـٰتِهِۦ وَيُزَكِّيہِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَـٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ “Shi ne (Allah) Wanda Ya aika, a cikin mabiya al’adu (marasa rubutu da karatu), wani Manzo daga gare su yana karanta ayoyinSa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar dasu Littafin da hikima ko da yake sun kasance daga gabaninsa lallai suna a cikin bata bayyananne”. ...