Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya
UMMU ADIYYA AL-ANSARIYYA "Ta halacci yakoki bakwai tare da Manzon Allah" - Mausu’ at Hayatis-sahabiyyat Sunanta Nusaiba bnt Haris ( نسيبة بن حارث ), a wata fadar kuma bnt Ka’ab (بنت كعب ) . Amma Abu Amr ya musunta hakan yace Nusaiba bnt Ka’ab ( نسيبة بنت كعب ) ita ce Ummu Ammara ( أم عمارة ), amma ita wannan an fi saninta da Ummu Adiyya ( أم عادية الأنصارية ). - Al-Isabah 8/437 Ibn Sa ’ ad yace "Ummu Adiyya ta musulunta tun da wuri kuma ta halacci yakoki da masu yawa tare da manzon Allah. Kuma ta ruwaici hadisai masu yawa daga gareShi". - Dabakaat, 455 An ruwaito daga wajenta tana cewa " Na halacci yakoki bakwai (7) tare da Manzon Allah ﷺ mun kasance muna dafa musu abinci, kuma muna kula da abin hawansu tare da yin magani ga wadanda aka yi wa rauni muna kuma jinyarsu " - Mausu at Hayatis sahabiyyat Imamuz-Zahabiy yace " Ummu Adiyya tana cikin mafiya sani cikin sahabbai ta ruwaito hadisai masu yawa ...