Posts

Showing posts with the label Aqeedah

Maganganun Malamai akan Mummunar Akidar Shia

Image
MAGANGANUN MALAMAI AKAN MUMMUNAR AKIDAR SHI'AH GA KADAN DAGA CIKI NA FARKO: IMAM MALIK BN ANAS An ruwaitu daga Imam Malik yace: " Wanda yake zagin sahabban Manzon Allah bai da rabo ko kuma cewa ya yi bai da kaso a cikin Musulunci" Almajirin Imam Malik mai suna Ashhabu ya ce: An tambayi malik dangane da Rafilawa”. Sai ya ce "kada ka yi magana da su kuma kada ka karbi ruwaya daga wurinsu domin suna yin Karya”. - Minhajus Sunnatun Nabawiyya 1/26 NA BIYU: IMAM SHAFI'I Ruwaya ta inganta daga gare shi ya ce " A cikin 'yan bidi a kaf ban taba ganin wanda ya fi Rafilawa karyaba da shaidar Zur.” - Al-Inabatul Kubra 2/545 NA UKU: IMAM AHMAD An karbo daga Abdullah bin Ahmad ya ce: “ Na tambayi babana dangane da mutumin da yake zagi daya daga sahabban manzon Allah.” Sai yace " Bana ganin yana kan Musulumci”. -  Kitabus Sunnah 1/493 Kuma harwayau an tambaye shi dangane da mutumin da yake da makwafci Dan Shi'ah: ...

Danduba da Boka

Image
DANDUBA (ARRAF) DA BOKA 1. DAN DUBA (ARRAF ) Mai Duba, shi ne wanda yake da’awa sanin abin da ya buya (sirri) ta hanyar wasu abubuwa da suke gabata ya kafa dalili dasu a kan sanin abin da aka sace da wajen da abin ya bace yake da makamancin haka. 2. BOKA Boka kuwa, shi ne wanda yake bayar da labarin abin da zai zo nan gaba. A wani fadin kuma aka ce: shi ne wanda yake da’awar sanin abin da ke cikin zuciya ta hanyar sihiri da amfani da aljannu. ( أحاديث السحر والرقية فى الكتب والسنة: 90 ) . Abul Abbas Ibn Taimiyya yace: Al-arraf suna ne na Boka da mai ilimin taurari da mai duba (ta hanyar buga kasa) da makamancinsu, na wadanda suke magana a kan sanin al’amura ta wadannan hanyoyi. Kuma Ibn Abbas yace dangane da mutane masu ilimin hisabin haruffa kuma suke duba tafiyar taurari yace bana ganin wanda ya aikata wannan yana da wani rabo a gurin Allah. An karbo hadisi daga Abu Hurairah (RA), Manzon Allah (SAW): "اجتنبوا السبع الموبقات" قالو: يا...