Tarihin Sahabbai 10: 1. Muaz bin Jabal (R)

MU'AZ BIN JABAL ( معاذ بن جبل ) "... وأعلمهم بالحلال والحرم معاذ " "Mafi sanin Al'umma halal da haram shi ne Mu'az bin Jabal" - Tirmizi 3793, Ahmad 3/184 Sunansa Mu'az bn Jabal bn Amr bn Aus bn A'iz bn Ka,ab. Ana yi masa alkunya da Abu Abdurrahman Al'khazrajiy Al'Ansariy (duba Al Isaiah). Ya halarci caffar A ƙ aba tare da mutanen madina a lokacin da aka yi Hijirah zuwa Madina, Manzon Allah ﷺ Ya hada shi 'yan uwantaka da Abdullah bin Mas'ud , ko da yake Ibn Ishaq ya ce 'an hada shi ne da Ja'afar bin Abi Talib ’. Ya halacci yakin Badar da dukkanin yakoki tare da Manzon Allah (duba Bidaya) A shekara ta tara da Hijira, Manzon Allah ya tura shi zuwa kasar Yamen domim ya koyar dasu Addinin musulunci, Mu'az bai dawo ba sai da Manzon Allah ﷺ Ya rasu. Taswirar Sham (Syria) Mu'az yana daga cikin manyan sahabbai da suka samu fahimtar Addini. Abdullah dan Umar yana cewa Manzon Alla...