Danduba da Boka

DANDUBA (ARRAF) DA BOKA 1. DAN DUBA (ARRAF ) Mai Duba, shi ne wanda yake da’awa sanin abin da ya buya (sirri) ta hanyar wasu abubuwa da suke gabata ya kafa dalili dasu a kan sanin abin da aka sace da wajen da abin ya bace yake da makamancin haka. 2. BOKA Boka kuwa, shi ne wanda yake bayar da labarin abin da zai zo nan gaba. A wani fadin kuma aka ce: shi ne wanda yake da’awar sanin abin da ke cikin zuciya ta hanyar sihiri da amfani da aljannu. ( أحاديث السحر والرقية فى الكتب والسنة: 90 ) . Abul Abbas Ibn Taimiyya yace: Al-arraf suna ne na Boka da mai ilimin taurari da mai duba (ta hanyar buga kasa) da makamancinsu, na wadanda suke magana a kan sanin al’amura ta wadannan hanyoyi. Kuma Ibn Abbas yace dangane da mutane masu ilimin hisabin haruffa kuma suke duba tafiyar taurari yace bana ganin wanda ya aikata wannan yana da wani rabo a gurin Allah. An karbo hadisi daga Abu Hurairah (RA), Manzon Allah (SAW): "اجتنبوا السبع الموبقات" قالو: يا...