Posts

Showing posts with the label Hadith

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Image
SAHABBAI 12 DA AKA FI RUWAITO HADISAN ANNABI (S.A.W) DAGA GARESU 1. ABU HURAIRAH (R.A.) A n ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 5374 daga gareshi 2. ABDULLAHI IBN UMAR (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 2630 daga gareshi 3. ANAS IBN MALIK (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 2286 daga gareshi 4. A’ISHA BINT ABUBAKAR (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 2210 daga gareta 5. ABDULLAHI IBN ABBAS (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 1660 daga gareshi 6. JABIR IBN ABDULLAHI An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 1540 daga gareshi 7. ABU SA’ID AL-KHUDRI (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 1170 daga gareshi 8. ABDULLAHI IBN MAS’UD (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 748 daga gareshi 9. ABDULLAHI IBN ‘AMR IBN ‘AAS (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 700 daga gareshi 10. UMAR IBN AL-KHATTAB (R.A.) An ruwaito hadisan Annabi (S.A.W.) 537 daga gareshi 11. ALIYU IBN ABU TALIB (R.A....

Sharhin Littafin Arabaeenan Nawawi - Gabatarwa

Image
SHARHIN LITTAFIN HADISIN ARBA’EENAN-NAWAWI ( شرح الكتاب الأربعين النووية ) Na Nana A’isha Muhammad  GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T.), Mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Habibinmu Abin koyinmu Muhammad ( Salaawatullahi alayhi) da alayensa da sahabbansa adalai da wadanda suke koyi da bin tafarkinsa har izuwa ranar sakamako. Hakika Allah Madukakin Sarki Yana cewa a cikin Alkur’ani, Suratul Juma’a aya ta 2:   هُوَ ٱلَّذِى بَعَثَ فِى ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ رَسُولاً مِّنۡہُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡہِمۡ ءَايَـٰتِهِۦ وَيُزَكِّيہِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَـٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ ۝ “Shi ne (Allah) Wanda Ya aika, a cikin mabiya al’adu (marasa rubutu da karatu), wani Manzo daga gare su yana karanta ayoyinSa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar dasu Littafin da hikima ko da yake sun kasance daga gabaninsa lallai suna a cikin bata bayyananne”. ...

Sharhin Littafin Arabaeenan Nawawi - Abubuwan da suke ciki

Image
SHARHIN LITTAFIN HADISIN ARBA’EENAN-NAWAWI ( شرح الأربعين النووية ) Na Nana A’isha Muhammad Assalamu Alaikum , Muna masu godiya ga Allah, da kuma farin cikin sanar da shiri da ‘yar uwa (Nana A’isha) ta dauki nauyi aiwatar da shi na Sharhin Hadisai Arba’in da biyu na cikin littafin Arba’inan-Nawawi . Nana ta taba rubuta Shuruh akan littafin Arba’unan Nawawi a Litinin 28th Safar, 1438 AH (28th November, 2016 AD) har izuwa ranar Juma’ah 13th Jumada Al-Awwal, 1438 AH (10th February, 2017 AD/CE), wanda ba a sami damar karasawa gaba-daya ba saboda dalilai na tafiya karatu dss. A wannan karon kuwa, in shaa Allah za a dawo tun daga farko har izuwa karshe tare da ‘yan gyare-gyare (editing) da kuma ‘yan kare-kare na Sharhi akan rubutun farko lokaci-zuwa-lokaci cikin yardarm Allah. Group Management ABUBUWAN DA SUKE CIKI 1. Sharhin Littafin Arba’una an-Nawawi 2. Abubuwan da suke ciki 3. Sadaukarwa 4. Gabatarwa 5. Takaitaccen tarihin marubu...