Tarihin Sahabbai 10: 1. Muaz bin Jabal (R)

MU'AZ BIN JABAL (معاذ بن جبل)
"...وأعلمهم بالحلال والحرم معاذ"
"Mafi sanin Al'umma halal da haram shi ne Mu'az bin Jabal"
- Tirmizi 3793, Ahmad 3/184





Sunansa Mu'az bn Jabal bn Amr bn Aus bn A'iz bn Ka,ab. Ana yi masa alkunya da Abu Abdurrahman Al'khazrajiy Al'Ansariy (duba Al Isaiah).

Ya halarci caffar Aƙaba tare da mutanen madina a lokacin da aka yi Hijirah zuwa Madina, Manzon Allah   Ya hada shi 'yan uwantaka da Abdullah bin Mas'ud, ko da yake Ibn Ishaq ya ce 'an hada shi ne da Ja'afar bin Abi Talib’.

Ya halacci yakin Badar da dukkanin yakoki tare da Manzon Allah (duba Bidaya)
A shekara ta tara da Hijira, Manzon Allah ya tura shi zuwa kasar Yamen domim ya koyar dasu Addinin musulunci, Mu'az bai dawo ba sai da Manzon Allah   Ya rasu.

Taswirar Sham (Syria)

Mu'az yana daga cikin manyan sahabbai da suka samu fahimtar Addini. Abdullah dan Umar yana cewa Manzon Allah yace:

"خذوا القرآن من أربعة:  من ابن مسعود، وأبيّ، ومعاذ بن جبل، وسالم مولى أبي حذيفة"

"Ku koyi karatun Alqur'ani daga mutane hudu; Abdullah bin Mas'ud,  da Ubayyu bin Ka,ab, da Mu'az bin Jabal da Salim Maula Abu Huzaifah"


Mu'az ya rasu a annobar da ta sami musulmi a kasar Sham (Syria a yanzu) a shekarata ta sha takwas 18 bayan Hijirah yana tare da Abu Ubaidah Amir bn Jarrah (R.A.) a lokacin yana da shekara 33 ko da hudu
- duba Al-Muntazam 4/365,  خلق المسلم للغزالي: ص١٣١، الطبقات لابن سعد ٣/١٢٤


Kabarin Sahabi, Muaz bin Jabal a Jordan

Allah kaqara mana son sahabban Manzon Allah ka tashemu tare dasu kacire mana duk wani gilli.
To be continue...  in shaa Allah.


20th Muharram, 1438AH
11th October, 2017CE

Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 1: Maimunatu bint al-Harith (R)