Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya


UMMU ADIYYA AL-ANSARIYYA
"Ta halacci yakoki bakwai tare da Manzon Allah"
- Mausu’ at Hayatis-sahabiyyat


Sunanta Nusaiba bnt Haris (نسيبة بن حارث), a wata fadar kuma bnt Ka’ab (بنت كعب). Amma Abu Amr ya musunta hakan yace Nusaiba bnt Ka’ab (نسيبة بنت كعب) ita ce Ummu Ammara (أم عمارة), amma ita wannan an fi saninta da Ummu Adiyya (أم عادية الأنصارية).
- Al-Isabah 8/437

Ibn Saad yace "Ummu Adiyya ta musulunta tun da wuri kuma ta halacci yakoki da masu yawa tare da manzon Allah. Kuma ta ruwaici hadisai masu yawa daga gareShi".
- Dabakaat, 455

An ruwaito daga wajenta tana cewa "Na halacci yakoki bakwai (7) tare da Manzon Allah ﷺ        mun kasance muna dafa musu abinci, kuma muna kula da abin hawansu tare da yin magani ga wadanda aka yi wa rauni muna kuma jinyarsu"
- Mausu at Hayatis sahabiyyat

Imamuz-Zahabiy yace "Ummu Adiyya tana cikin mafiya sani cikin sahabbai ta ruwaito hadisai masu yawa"
- Siyaru 2/318

Lokacin da 'yar Manzon Allah  ta rasu, wato Zainab Ummu Adiyya tana cikin wadanda suka yi mata wanka kamar yadda Muhammad bin Sirina ya ruwaito daga gareta tana cewa:

"Manzon Allah  ya shiga wurinmu yayin da 'yarsa Zainab ta rasu sai yace :

اغْسِلْنَهَا ثَلاَثًا أَوْ خَمْسًا أَوْ أَكْثَرَ مَنْ ذَلِكَ إِنْ رَأَيْتُنَّ ذَلِكَ بِمَاءٍ وَسِدْرٍ، وَاجْعَلْنَ فِي الآخِرَةِ كَافُورًا أَوْ شَيْئًا مِنْ كَافُورٍ، فَإِذَا فَرَغْتُنَّ فَآذِنَّنِي. فَلَمَّا فَرَغْنَا آذَنَّاهُ فَأَعْطَانَا حِقْوَهُ فَقَالَ ‏"‏ أَشْعِرْنَهَا إِيَّاهُ ‏"‏‏.‏ تَعْنِي إِزَارَهُ‏.

"ku wanke ta sau uku (3) ko sau biyar (5) ko fiye da haka idan kun so da ruwa da magarya a karshen wankewar ku sanya kafur ko wani abu daga kafur in dai kun gama ku gaya minta ce: "Ya yin da muka gama sai muka gaya masa sai ya bamu mayafinsa" Yace "ku lullubeta da shi"
- Bukhari 1253, Muslim 939

An ce Ummu Adiyya  Mace ce mai yawan kyauta da sadaka da taimakon raunana.

An ce bayan wafatin Manzon Allah, Ummu Adiyya ta tashi daga madina ta koma Basra. An ruwaito cewa khalifa Aliya Bin Abi Dalib har yakan yawan ziyararta a gidanta har ya kwanata ya yi kailula a gidanta.


26th Muharram, 1439AH
(17th October, 2017CE)

Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi