Tarihin Sahabbai Mata 2: Ummu Rumana
UMMU RUMANA
AL-KINANIYAH
(أم رومان الكنانیة)
Sunanta Ummu Rumana bint Amir ibn Umaymir bn Abdulsham ibn Attab ibn Uzaifah ibn Subi'i bn Duhman ibn al-Haris ibn Ghanam ibn Malik ibn Kinana (رضي الله عنھا و أرضاھا). Ita ‘yace ga ‘Amir ibn Umaymir wanda su Banu Kinanahne. Sunan na asali shi ne Zainab kamar yadda aka ruwaito daga Ibn Ishaq.
- Al’isaba
8/391
Ummu Rumana ta
kasance mata gun Khalifan Manzon Allah ﷺ Abubakar as-Siddiq (R), kuma mahaifiya ga Nana A’isha da
AbdurRahman bin Abubakar Assiddiq. Ana mata kirari da cewa "Duk
wanda yake son ya ga Hurul'ini tun a duniya to ya dubi Ummu Rumana".
- Tahzibul
Kamal 35/259
A zamanin
jahiliyya ta auri wani da ake kira Al-Haris bn Sakhbarah (الحارث بن سخبرة) ta Haifa masa al-Dufail. Bayan rasuwarsa
sai ta auri Abubakar As-Siddiq (R). Ta musulunta tun da wuri ta mika wuya ga
manzon Allah, sannan ta yi hijira zuwa Madina tare da Iyalan Gidan Manzon Allah
ﷺ da 'ya'yanta da dukkan iyalan Abubakar, Allah Ya kara musu
yarda.
- At-Tabaqaat
8/276
Ummu Rumana ta
kasance salaha, mutumiyar kirki abar kwatance.
Ummu Rumana ta
rasu a zamanin Manzon Allah ﷺ a watan Dhul-Hijja
shekara ta shida (6) bayan Hijira a , an ce ya yin da ta rasu Manzon Allah ﷺ ne ya shiga
cikin kabarinta, sannan ya ce:
"من سره أن ينظر إلى امرة
من الحور العين فلينظر إلى أم رومان"
“WANDA DUK YAKE
SO YA GA HURUL-INI TUN A DUNIYA TO YA DUBI UMMU RUMANA”. Sannan Manzon Allah ﷺ Ya nema mata gafara.
- Al-Isaba
8/391, Musnad 6/212, Ibn Hajar a Fathul-Bari 7/438; da Mausu'at Hayatis Sahabiyyat.
Ka’ab Saleh
Abdulkarim
24th Muharram,
1439AH
15th October,
2017CE
Comments
Post a Comment