Me Yasa Yansanda (POLICE) basa Yafe Laifi?



HAƘƘINMU DA HAƘƘIN HUKUMA

…tafe yake yana ta surutai shi kaɗai alamu dai yana cikin damuwa da ɓacin rai bayan dawowarsa daga Ofishin ‘Yan Sanda (Charge Office/Police Station); “Me ya farune, kai kaɗai kana ta surfa masifa?” na tambayeshi cikin zumuɗi.

Sai ya amsa min da cewa:
Wannan yaronne ɗan gidan Marigayi wanda ya sace min Laptop, wayata da kuma ƴan chanjikana (kuɗaɗe), mun je wajen ‘yan sanda an dawo min da Laptop da Wayar amma kuɗin wai babu su har ya kashe; sai nace Alhamdulillah ya je tunda mafiya muhimmanci sun dawo na yafe masa kuɗin a sake shi kurum. Wai sai hukumar ‘yan sandar suka ce ai su basu yafe ba, kai ka ji fa! Ni da aka yiwa laifi na yafe amma sai sun yi halinnasu na ‘yan sanda”.

Na yi dariya nace masa: “Don me za su yafe masa? Ba laifi yayi ba?”

Yace: “Na ga laifin nan ni ya yiwa, ko?”

Nace: “Hakane, anyi maka laifi, ya kuma yiwa hukuma laifi. Kai ka yafe naka an kuma dawo maka da haƙƙinka, saura ita hukuma zata nauki mataki na haƙƙintane ita ma, saboda an samu intersection tsakanin laifin da aka maka (ɗauka maka dukiyarka) da laifi na sata wanda ya saɓawa doka.”

Abin da yake faruwa shi ne; akwai haƙƙoƙi biyune kenan cikin lamarinka wato Civil (haƙƙin mutum ɗaya tilo) da kuma Crime (Karya dokar hukuma) saboda ya against Public Law (Penal Code). Idan kai ɗaya da aka yiwa laifin sata an dawo maka da haƙƙinka na kayan da aka sace  (restitution) an fita naka haƙƙin. Ita ma hukuma da yake ta haramta ta kuma cewa duk wanda ya karya mata doka ga hukunci da za a masa (don ta tabbatar ɗa'a da kwanciyar hankalin al'umma) haƙƙintane idan wani ya saɓa doka ta masa adalci (hukunci); ka ga an sami aure tsakanin Civil da Crime kenan (intersection). Domin yana daga cikin primary roles na ‘yansanda na tarbiyantar da al’umma, tabbatar da doka da filing case zuwa kotu (as prosecutor/prosecution counsel).

Shi yasa wajen da kace ka yafe ita kuma hukuma tace bata yafe ba, saboda wadancan dalilan na sama. Laifin sata is non-compoundable offence (Laifine da in wanda aka yiwa laifi 'plaintiff' yace yafe sai hukuma ta ɗauki mataki na karya dokar ƙasa da mai laifi yayi 'criminal') da dangi ire-iren wannan kamar yadda suke a APPENDIX (A) na Criminal Procedure Code (CPC).



Amma da a ce baka kai shi ƙara wajen yan sanda ba, sai kuka kashe case ɗinku a gida, ya dawo maka da kayanka babu ruwan ‘yansanda da kai sai dai idan kayi karanbanin ɗaukar matakin hukunci da hannunka; wannan ko a wajen shari’un Musulunci haka abin yake kamar fadin Aljaza’iry:

إذا عفا صاحب المال عن الساق ولم يرفعه إلى السلطان فلا قطع، وإن رفعه إليه وجب القطع ولم تنفعه شفاعة أحد بعد ذلك


25th D/Qa'adah, 1438AH
(Thu. 17th August, 2017CE)

Comments

Popular posts from this blog

Tarihin Sahabbai Mata 1: Maimunatu bint al-Harith (R)

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai 10: 1. Muaz bin Jabal (R)