Maganganun Malamai akan Mummunar Akidar Shia

MAGANGANUN MALAMAI AKAN MUMMUNAR AKIDAR SHI'AH
GA KADAN DAGA CIKI

NA FARKO: IMAM MALIK BN ANAS
An ruwaitu daga Imam Malik yace: "Wanda yake zagin sahabban Manzon Allah bai da rabo ko kuma cewa ya yi bai da kaso a cikin Musulunci"

Almajirin Imam Malik mai suna Ashhabu ya ce: An tambayi malik dangane da Rafilawa”. Sai ya ce "kada ka yi magana da su kuma kada ka karbi ruwaya daga wurinsu domin suna yin Karya”.
- Minhajus Sunnatun Nabawiyya 1/26

NA BIYU: IMAM SHAFI'I
Ruwaya ta inganta daga gare shi ya ce "A cikin 'yan bidi a kaf ban taba ganin wanda ya fi Rafilawa karyaba da shaidar Zur.”
- Al-Inabatul Kubra 2/545

NA UKU: IMAM AHMAD
An karbo daga Abdullah bin Ahmad ya ce: “Na tambayi babana dangane da mutumin da yake zagi daya daga sahabban manzon Allah.” Sai yace "Bana ganin yana kan Musulumci”.
-  Kitabus Sunnah 1/493

Kuma harwayau an tambaye shi dangane da mutumin da yake da makwafci Dan Shi'ah: Yana iya yi masa sallama? Sai ya ce "A'a, sam kuma idan shi ya yi masa sallama kada ya amsa."
- Kitabus Sunnah 1/494

NA HUDU: ALKALI IYAD ALMALIKIY
Wanda ya shahara da littafinsa Ashafa ()
Yana cewa:"Haka nan kuma muna yanke hukunci da kafircin gulatu Rafilawa wadanda suka ce Imamai sun fi Annabawa falala”.
- Ashifa 2/1078

NA BIYAR: IMAM DAHAWI
Ya fadi acikin Akidarsa kuma muna son sahabban manzon Allah ba ma takaitawa wajen son dayansu, kuma ba ma barranta daga dayansu, muna kin wanda yake kin su kuma yake ambaton su ba da alheri ba mu ba ma ambaton su sai da alheri. Mun kudure cewa sonsu addini ne da imani da ihsani kuma kinsu (kuma) kafirci ne da munafunci da zalunci”
- Al’akidatul Dahawiyya shafi na 689

NA SHIDA: IMAM AHMAD BIN ABDULHALIM BIN ABDULSALAM BIN TAIMIYYA
Yana cewa :"Allah ya sani kuma Allah ya isa masani cewa a cikin kungiyoyin bidi'ah duka masu danganta kansu da musulunci babu wanda ya fi su sharri da jahilci da karya da zulunci da sabo haka nan babu wanda ya fi su nisa da hakikanin imani wato Rafilawa”.
- Minhajus sunnah 1/160

NA BAKWAI: MUJADDADI DANFODIYO
Shi ne wanda akan sa zandakata shi.  Shi shaihu Usman Danfodiyo a zamanin sa babu su a kasar nan amma yana sane da su da miyagun akidojinsu bayan ya ruwaitu maganar Hafiz ibn Hajar inda yake cewa: "wanda duk ya kafirta sahabban ko ya ce al'umma ta bata to shi kafiri ne" sai ya ce "Na ce haka nan duk wanda ya yi shakkar kafircinsa shi ma kafiri ne."

Dubi yadda Shaihu Mujaddadi ya kafirta mai shakkun kafircin Dan Shi'ah ta hakane za ka Fahimci cewa kafircin 'yan Shi'ah yana da kaushi ainun.

Allah Ka karemu daga wannan mummunar akidar, amin.

Mal. Ka'ab Saleh
24th Muharram, 1439AH

15th October, 2017CE

Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya

Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi