Kaidojin Tafikar da Alamuran Group na Darul Uloom

KA’IDOJIN TAFIKAR DA AL’AMURAN
GROUP NA DARUL ULOOM





بِسْـــــمِ اللَّـــهِ الرَّحْــــمَٰنِ الرَّحـــِيم

Waɗannan sune ƙa'idoji da aka gina domin tafikar da tsarin wannan Zauren, domin ayi komai bisa tsari.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••المسلمون على شروطهم -  الترمذي، 1352
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

 1 |. Ba'a saka mutum a wannan group ɗin, sai wanda ya nuna sha'awar shiga. Sannan zai turo da cikekken sunansa (full name), lambarsa ta Whatsapp, da fannin (course) da ya/yake karanta.

 2 |. Kowanne member yana da damar (right) na yin posting abubuwan da suka shafi ilimai (علوم) daban-daban waɗanda suka haɗa dana fannonin Addini (Religious), Kimiyya da Fasaha (Science & Technology), Tarihi (History) da Yare (Linguistics) Zamantakewa da sauransu.

 3 |. Yana da kyau idan zaka turo photo ko video, ya rubuta abin da ke kunshe a cikinsu a taƙaice (briefly).  Sannan idan kai ka rubuta abu yana da kyau ka duba sosai kafin turo.  Hakanan idan kwafowa ka yi a wani waje yana da kyau ka ƙara duba sahihancin posting ɗin kafin ka turo.

 4 |. Haramun ne member ya turo da posting, ko turo photo ko video da ya shafi wasanni (sport), tallace-tallace (adverts), labarun ban-dariya na ƙarya (jokes), jita-jita (rumors & gossip), fini-finai (films), ƙazafi (slander), batsa (porn), ko posting akan magungunan mata a group ɗin maza, ko na siyasa (politics) sai in na ilimi siyasane (Political Studies/علوم السياسية), ko posting mai ƙa'ida (wato ace sai an turawa mutum kaza ko abu kaza ya sami mutum) ko duk wani posting da ya saɓawa ilimi ko wanda zai kawo mana hargitsi (nuisance) a cikin group.

 5 |. Ba'a hira (chatting) ko soyayya (dating) a cikin group domin ba da wadannan manufofi (aims/objectives) aka ƙirƙiri shi wannan group ɗin ba.  Ba'a gaishe-gaishe, ko turo da Sallama ba tare da dalili ba, sai dai in posting mutum zai yi, saboda da gudun buɗƙofar yin hira (chatting) a group.

 6 |. Darul Uloom ba group din Malamai ba ne, na ɗalibaine, don haka ba'a karambanin bada Fatawa (basa amsa cikin masa’il na addini). Amma kana iya turo da tambaya da ta shafi kowanne fanni (fields) idan da wanda abin ya shafi ɓangarensa sai ya amsa maka.  Sannan idan wani yayi posting idan akwai abin da baka gane ba cikin posting ɗinsa ba, sai ka bishi ta private ka tambayeshi ya ƙara maka bayani.

 7 |. Lokaci-zuwa-lokaci (time to time) muna da ware lokuta da ake muhawara (debate), tattaunawa (discussion) da kacici-kacici (quiz) akan ilimai (علوم) ko zamantakewa da mu'amala ta yau da kullum. Wanda kowanne ɗan cikin group (member) yana damar a dama da shi cikin waɗannan shirye-shirye a lokutan da group ya ware.

 8 |. Idan da mai neman ƙarin bayani (info), ƙorafi (fussing), ko son bada wata shawara (suggestion) ko ƙarin hasken akan al'amuran group, a kullum ƙofarmu a buɗe ta ke.

 9 |. Duk wanda ya karya ɗaya ko dukkan waɗannan ƙa'idoji da aka zayyano, za a cire (removing) mutum, kuma ba za a adding mutum ba, har sai ya turo da saƙon bada haƙuri (apology note) bisa kuskuren da yi da kwana uku.

Da fatan za a ba mu haɗin kai, domin ci gabanmu baki ɗaya

©DARUL ULOOM
WHATSAPP GROUP

Comments

  1. السلام عليكم ورحمة الله
    A gaskiya naji dadin wannan tsari naku qwarai da gaska, Allah ya karbi wannan qoqari naku ya dora maku shi a mizanin kyawawan ayyukanku.
    Ga lambata ta whatsapp ina roqon a sakani cikin wannan group mai albarka.
    07064580866,

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Tarihin Sahabbai Mata 1: Maimunatu bint al-Harith (R)

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai 10: 1. Muaz bin Jabal (R)