Danduba da Boka

DANDUBA (ARRAF)
DA BOKA

1. DAN DUBA (ARRAF )
Mai Duba, shi ne wanda yake da’awa sanin abin da ya buya (sirri) ta hanyar wasu abubuwa da suke gabata ya kafa dalili dasu a kan sanin abin da aka sace da wajen da abin ya bace yake da makamancin haka.

2. BOKA
Boka kuwa, shi ne wanda yake bayar da labarin abin da zai zo nan gaba. A wani fadin kuma aka ce: shi ne wanda yake da’awar sanin abin da ke cikin zuciya ta hanyar sihiri da amfani da aljannu. (أحاديث السحر والرقية فى الكتب والسنة: 90).

Abul Abbas Ibn Taimiyya yace: Al-arraf suna ne na Boka da mai ilimin taurari da mai duba (ta hanyar buga kasa) da makamancinsu, na wadanda suke magana a kan sanin al’amura ta wadannan hanyoyi. Kuma Ibn Abbas yace dangane da mutane masu ilimin hisabin haruffa kuma suke duba tafiyar taurari yace bana ganin wanda ya aikata wannan yana da wani rabo a gurin Allah.


An karbo hadisi daga Abu Hurairah (RA), Manzon Allah (SAW):

"اجتنبوا السبع الموبقات" قالو: يا رسول الله وما من؟ قال: "الشرك بالله، والسحر، وقتل النفس التى حرم إلا بالحق، وأكل الربا، وأكل مال اليتيم والتولي يوم الزحف، وقذف الحصنات المؤمنات الغافلات"

“Ku nesanci abubuwa masu halakarwa guda bakwai, sai akace ya Manzon Allah mene ne su? Ya ce, Tarayya da Allah, da Sihiri (zuwa gun boka, ko yin tsafi), da kisan kai wanda Allah Ya haramta, sai da gaskiya, da cin dukiyar marayu, da cin Riba, da juya baya a fagen yaki (watau gudu), da karya (kage) wa muminan mata tsararru (masu kamun kai) wadanda suka tsare kansu.
-  Fathul Bari 3/62

MENENE HUKUNCIN WANDA YAJE WAJAN BOKA
Hadisi ya tabbata acikin Sahihu muslim.
Manzon Allah yace "Duk wanda ya Je gurin boka ya tambaye shi wani abu kuma ya gaskata abin da ya ba shi labari to ba za a karbi sallarsa ta kwana arba, in ba "
Da hadisin Abu Hurairah (R.A.) daga Manzon Allah yace:

" من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد".
"Duk wanda ya je gurin boka kuma ya gaskata abin da yake fadi to hakika ya kafircewa Abin da aka saukar wa manzon Allah "
- Targhib 4/53: Abu Dauda, Ibn  Majah, Tirmidhi da Hakim su ne suka ruwaito

A wata ruwayar ma, ba za a karbi ibadar mutum ba ta kwanaki arba’in (40), da makamantan irin wannan hadisai wanda suke tsoratar damu zuwa wajan boka ko danduba Allah kakara shiryar damu akan bin sunnar manzon ka kakara nesantamu daga wadannan mutanen masu wannan halaye, Allah kabamu ikon bin gaskiya da kuma aiki da ita.

خير الكلام من قل ودل، سبحانك اللهم وبحمدك، أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك

22nd Muharamma, 1438AH

(10th October, 2017CE)

Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya

Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi