Chanja Sunan Group daga LET ME LEARN zuwa DARUL ULOOM

CHANJA SUNAN GROUP
       ZUWA DARULULOOM        
19011439AH | 10102017CE
Assalamu Alaikum

Group ɗin LET ME LEARN an ƙirƙireshi tun ranar 19th April, 2015 (shekara 2 da watannin 4 da sati 2 da kwanaki 3 a yau), wanda a tsari na Onomastic, an haɗa sunan group ɗin da kalmomin Turanci guda uku LET, ME da kuma LEARN wanda ke nufi BAR NI IN KOYA/SANI a Hausance. Muna gudanar da harkokin group da suka shafi ilimi zalla a cikin group ɗaya (1), daga baya da mutane suka yi yawa (group ɗin ya cika) sai aka buɗe Group 2, aka buɗe Group 3 (na mata), wanda a yanzu haka group yana da members guda 340 (Group 1: 172, Group 2: 72 & Group 3: 96).Bayan karɓar shawarwari daga ƴan uwan, yayu kuma iyaye masana masu nazari akan sanya suna da alaƙa (Onomatology/علم الأسامي) da kuma tsarin ƙungiyoyi (I/O Psychology/الحالة العاطفية الجماعية) wajen sabunta sunan group/المجموع ya koma wanda zai haɗa kowannen ɓangare (na malamai da almajirai) da masu nazariyyat daban-daban bisa hujjoji na ilimi (Textual proofs/الأدلة النقلية) da na hankali (Rational Proofs/الأدلة العقلية) da kuma nazari abin da hakan zai haifar ana gaba (Futurology/علم المستقبلياتا) in shaa Allah.


DARUL ULOOM
DARUL ULOOM (دار العلوم) kalmomin larabci ne biyu  (compound; دار da kuma العلوم). DAARUN (دارٌ) a yare yana nufin gida (house), AL-ULOOM (العلوم) jam’in (plural) kalmar ILM (علمٌ), ma’ana ilimi/sani. Idan muka hadesu za su ba mu DARUL-ULOOM (Gidan Ilimi/House of Knowledge) kuma shi ne sunan da muka zaɓa domin sabunta (change of name/تغيير الاسم) na group ɗin LET ME LEARN, kuma in shaa Allah dukkan posting ɗinmu na gaba (future postings) za suna fita da sunan DARUL ULOOM .

Daga cikin sauye-saye na cigaba da muka samu, mun buɗe blogsite na kamfani google, page a shafin Facebook, shafi a Manhajar Twitter, Group a Manhajar Telegram da kuma shafi a Google+. Sannan a jiya an buɗe sabon Email na group.

Daga cikin sabbin tsare-tsaren group, akwai haɗa kacici-kacici (Quiz/المسابقة), filin muharawara da tattaunawa (debate & discussion/المناقشة) kan wasu masa'il na rayuwa ko na addini da sauraransu lokaci-zuwa-lokaci in shaa Allah.

A ƙarshen muna fata da kuma roƙon Allah Ya sakawa kowa da alkhairi, Ya ƙara sanya mana albarka cikin rayuwarmu musamman ta ɓangaren karatu, Ya bamu iko da dama amfana da duk wani tsari da aka kawo mana na cigaba amin

Signed:
Management
Whatsapp Group
19th Muharamma, 1439AH
10th October, 2017CE


   


Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya

Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi