Sharuddan Kalmar Shahada

SHARUDDAN
KALMAR SHAHADA
- Nana A’isha Muhammad


Kalmar Shahada ita ce La’ilaha illal-laah  (Ma’ana Babu abin bauta da gaskiya sai Allah), wa anna Muhammadar Rasulullah (kuma Annabi Muhammad (S.A.W.) Manzon Allah ne), ga wanda ya fadi wannan kalma yana mai imani da ita ya Musuluta (ma’ana ya mika wuya izuwa ga addinin Allah i.e. Musulunci).

Amma fadin wannan kalma da baki baya isarwa mutum, har sai ya cika sharuddanta kamar haka (a takaice):

A. ILIMI;
Ma’ana dole ka nemi ilimin sanin hakikanin ma’anar Kalmar, kamar yadda Allahu (S.W.T.) Ya fadi a cikin Al-Qur’ani Maigirma, Suratul Muhammad aya ta 19:

فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُ ۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَٮٰكُمۡ

Babu yadda za a yi mutum ya yiwa Allah wata bauta face yana da ilimin sanin yadda ake yinta, haka mutum Musulmi ba zai yi magana game da Allah ko abin da ya shafi Addininsa ba face mutum yana da sanin abun a ilmance.

B. YAQINI:
Ma’ana yarda da kuma barin kwokwanto game da lamarin Allah da kuma addininsa, da yarda da kuma jingina lamari zuwa gareShi ba tare da jin wani dar-dar a zuciya ba. Misali Suratul Hujura aya ta 15.

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمۡ يَرۡتَابُواْ وَجَـٰهَدُواْ بِأَمۡوَٲلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِۚ أُوْلَـٰٓٮِٕكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ ۝

C. QABUL:
Ma’ana amsar ko karbar duk wani abu da Allah Yace ayi ko Yace a bari gaba daya, ba tare da mutum ya ware abin da yake so ba, Misali fadin Allah (S.W.T.) a cikin Suratul Baqarah aya ta 85.

D. AL-INQIYAD:
Ma’ana meka wuya, idan an ce mai ka wuya shi ne ka daba kanka gaba daya ga Allah, duk abin da Allah Yace ko Manzonsa (S.A.W.) Yace ba kai ba jayayya akan wannan abin, ko da kuwa ya tsabawa tunaninka (sai mutum ya je nemi ilimi domin ya cirewa kansa kokwanto), dole ka yarda ka bi, ko da kana aikata wani abu idan aka ce Allah ya hana, dole ka hanu ka maika wuya, ka gujewa son zuciya. Misali Suratul Nisa’i aya ta 65.

فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِىٓ أَنفُسِہِمۡ حَرَجًا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا ۝

E. AL-SIDQ:
Ma’ana gaskatawa, kishiyar munafurci ko karyatawa, mutum Musulmi ya kasance ya kakkabe duk wani munafurci dake cikin zuciyarsa tsakaninsa da addinin Allah. Misali Suratul Baqarah aya ta 1-8.

F. IKLASI:
Ma’ana yi ko aikata wani aiki domin Allah, mutum Musulmi ya kasance duk abin da ya shafi addinin Allah ya yi shi da zuciya daya, da  kuma Iklasi (ma’ana yi don Allah) ba tare da ya sanyawa zuciyarsa kishiyar hakan ba, ya guji Riya (yi don mutane), ko neman yabo da sauransu. Misali fadin Allah (S.W.T.) a cikin Suratul al-Bayyina aya ta 5.

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٲلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ ۝

G. MUHABBAH:
Ma’ana soyayya, dole mutumin da ya aminta da Kalmar shahada ya so Allah sama da komai, sannan duk abin da mutum zai so ya so wannan domin Allah, haka in zai ki shi. Manzon Allah (S.A.W.) Yace: “Duk wanda yake son ya sami dandanon Imani to so mutum ba don komai sai don Allah”. Sauran Misalai: Suratul Baqara aya ta 165; Suratut-Tawbah aya ta 24.

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادًا يُحِبُّونَہُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبًّا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ ۝

H. KAFURCEWA DAGUTI:
Ma’ana kin duk wani bauta koma bayan Allah, dole mutum Musulmi ya gujewa duk wani da zai zamatowa Allah kishiyane wajen bauta, misali Annabawa, Mala’iku, Gumaka, Shehunai, Waliyai, Shaidanu dss. Misali Suratul Baqara aya ta 256.

لآ إِكۡرَاهَ فِى ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَىِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّـٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ ۝

I. IMANI DA KUMA KAUNAR MANZON ALLAH (S.A.W.)
Dole ne duk wanda ya yarda da Kalmar Shahada yayi imani da Manzon Allah (S.A.W.), Ya gaskataShi, ya so shi fiye da kowa da komai a rayuwarsa, ya bi koyarwasa, ya hanu da haninsa. Duk wanda ya ji baya son Annabi (S.A.W.) ba shi imani, kuma dole son ya kasance fiye da son komai da rayuwar mutum. Misali Suratul Tawbah aya ta 24, Ahzab aya ta 21 dss.

قُلۡ إِن كَانَ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُڪُمۡ وَإِخۡوَٲنُكُمۡ وَأَزۡوَٲجُكُمۡ وَعَشِيرَتُكُمۡ وَأَمۡوَٲلٌ ٱقۡتَرَفۡتُمُوهَا وَتِجَـٰرَةٌ تَخۡشَوۡنَ كَسَادَهَا وَمَسَـٰكِنُ تَرۡضَوۡنَهَآ أَحَبَّ إِلَيۡڪُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادٍ فِى سَبِيلِهِۦ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِىَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَہۡدِى ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَـٰسِقِينَ ۝


J. Dole mutum musulmi yayi riko da Kalmar Shahada da dukkan sharudanta har ya koma ga Allah, wanda yayi haka shi ne ya rabauta. Misali Suratul ali-Imran aya ta 102.

يَـٰٓأَيُّہَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ ۝ وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُواْۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ كُنتُمۡ أَعۡدَآءً فَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم بِنِعۡمَتِهِۦۤ إِخۡوَٲنًا وَكُنتُمۡ عَلَىٰ شَفَا حُفۡرَةٍ مِّنَ ٱلنَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنۡہَاۗ كَذَٲلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَـٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَہۡتَدُونَ ۝

Ya Allah! Ka bamu ikon riko da bin addininKa yadda kake so, Ka kuma sanya Kalmar Shahada ta kasance kalmarmu ta karshe a yayin mutuwa amin.


25th Muharram, 1439AH

(16th October, 2017CE)

Comments

Popular posts from this blog

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya

Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi