Sharhin Littafin Arbaeenan Nawawi - Tarihin Imam anNawawi

SHARHIN
LITTAFIN HADISIN
ARBA’EENAN-NAWAWI
(شرح الكتاب الأربعين النووية)
Na
Nana A’isha MuhammadTAKAITACCEN TARIHIN IMAMUN-NAWAWI

SUNA DA NASABA

1. Suna
Sunansa Yahaya, dan Sharraf dan Moori dan Hassan dan Hussaini dan Muhammad dan Juma dan Hazm. Maihaifinsa (Sharraf) ya kasance babban dan kasuwa a garinsu na Nawa.

2. Alkunya
Ana yi masa Alkunya da Abu Zakariyya, amma Zakariyya ba dansa bane, Alkunyarsa ce haka kamar yadda ya radawa kansa hakan, domin shi (Imamun-Nawawi) bai taba yin Aure ba.

3. Sunan Girmamawa
Mutane suna bashi wani ‘title’ da Muhyuddin (ma’ana Mai raya Addini), saboda bada lokutansa da yayi na yiwa Addinin Musulunci hidima na karantarwa, rubuce-rubuce da wa’azi.

4. Laqabi
An-Nawawi, saboda da sunan garinsu Nawa

HAIHUWARSA
An haifi Imamun-Nawawi a watan Muharram a shekara ta 631 bayan Hijira (1234 AD), a garin Nawa () wani gari da yake kusa da Damascus babban birnin kasar Syria daga bangaren kudu.

TAFARKINSA DA AKIDARSA
Imam an-Nawawi mabiyin tafarkin Sunnahne (Sunni), ta bangaren aqida kuma yana bin Ash’ariyya (Ash’ari).

SIFFARSA
Imam an-Nawawi farin mutum ne, madaidaici a tsayi, yana da dogon gemu, fuskarsa tana cike da annuri, yana da sakin fuska (da murmushi), bai fiye son surutu ko yin sa ba. Imam yana kokarin fadar gaskiya a ko ina ne ga kowaye, ba shi da tsoro ka zargeshi indai yasan in ya fadi magana zata amfani mutane, ko kuma ta shafi hakkin Allah. Kamar yadda Imam al-Dhahabi ya fadi. Imamun-Nawawi ya kasance mutum mai kaifin kwakwalwa ta hadda, yana tafiyar da lokutansa na kowacce rana a nema da kuma bada ilimi.

RAYUWAR KARATUNSA
Ya fara karatunsa tun yana dan karami a cikin garinsu na Nawa, mahaifinsa kuma ya bashi gudunmawa kan ya nemi ilimi, duk da kasancewar suna kasuwanci (domin mahaifinsa dan kasuwa ne).

Sannan Imamun-Nawawi ya shiga makarantar Saaramiyah da Rawaahiya (wacce aka maida ta Ummvi University a yanzu) wadanda duk suke a kasar Damascus (babban birnin kasar Syria), a inda yayi karatu mai zurfi a bangaren ilimin harshen Larabci (Arabic), Hadisi, Fiqhu da suran ilimai na Shari’a, a inda Imam-Nawawi yake daukar darussa goma sha-biyu ko fiye a wajen Malamai daban-daban a kowacce rana a darussan da aka ambata a sama. Bayan ya dawo daga darasu yana zama a gida ya rubuce abin da ya koyo ya kuma kara nazarinsa.

Wasu daga cikin Malaman Imam an-Nawawi
1. Abdul Rahman al-Anbari
2. Abdul Rahman bin Ibrahim al-Fazari
3. Abdurrahaman bin Muhammad al-Maqdisi
4. Abu Ishaq Ibrahim al-Wasiti
5. Ahmad bin Salim Al-Misri
6. Ibrahim bin Abu Hafs Umar bin Mudar al-Mudari
7. Khalid bin Yusuf An-Nablusi
8. Sharafuffin Abdul-Aziz bin Muhammad al-Ansari

AIKIN KARANTARWA
Imam-An-Nawawi ya fara aikin koyarwa a makarantar Ashrafiyah wacce ita ma take a birnin Damascus a lokacin yana dan shekara 24 tun daga wannan shekara har izuwa mutuwarsa yana tafikar da lokutansa wajen neman ilimi da kuma karantarwa, a birnin Damascus.

Wasu daga cikin manyan almajiransa
1. Abul-Abbas Al-Ja’fari
2. Abul-Hajjaj Yusuf bin Az-Zaki
3. Alauddin bin Attar
4. Jamaluddin Sulaiman bin Umar Az-Zar’i
5. Rashid Isma’il Al-Hanafi, da sauransu

RUBUCE-RUBECENSA
Imamun-Nawawi yayi rubuce-rubuce da yawa domin ‘yan bayansa su amfana da baiwar da Allah ya masa ta ilimi musamma a bangaren ilmin Hadis da tarbiyya. Ga wasu daga cikin litattafansa (A-Z sorting):

1. Adab al-Fatwa wal Mufti wal Mustafti (آدب الفتوى والمفتي والمتفتى)
2. Adhkar (الأذكار المنتخبة سيد الأبرار)
3. Al Majmu Sharh al-Mu’ajam (المجموع شرح المهذب) (bai kammala shi ba Allah ya karbi rayuwarsa)
4. Al-Irshad wa’Taqrib fi Ulum al-Hadith ()
5. Al-Tibyan fi Adab Hamalatul Qur’a (التبيان فى آدب حملة القرآن)
6. Arba’inan-Nawawi (الأربعون النووية)
7. At-tahzib al-Asma (تهذيب الأسماء)
8. Ma Tamas Ilayhi hajat al-Qari li Sahihil Bukhari (ما تمس إليه حاجة القارى لصحيح البخارى)
9. Minhajul Talibin (منهاج الطالبين)
10. Muhimmatul-Ahkam ()
11. Raudatul Talibin ()
12. Riyadus-Salihin (رياض الصالين)
13. Sharhin littafin Sahih Muslim (شرح صحيح مسلم)
14. Sharhin Sunan Abi Dawud (شرح أبو داود)
15. Tabaqatush-Shafi’iyyah ()
16. Tahriul Tanbih (تحرير التنبه)
17. Taqribu wat Taysir (التقريب والتيسير)
18. Da sauransu wasu littafai wallafarsa….

WAFATINSA
Imamun-Nawawi ya bar duniya a ranar Asabat 27 ga watan Rajab, shekara ta 676 bayan Hijirar Annabi (SAW) daga Makkah zuwa Madinah, bayan dawowarsa gida (garinsu a 1278 AD) a lokacin da rashin lafiya ya dan tsananta gareshi. Imamun Nawawi ya rasu yana da shekara 46. Kuma ya rasu bai taba yin aure ba.

Allah Ya kara masa rahama, amin.

Nana A’isha Muhammad
1st Safar, 1439AH
(22nd October, 2017CE)

Comments

Popular posts from this blog

Tarihin Sahabbai Mata 1: Maimunatu bint al-Harith (R)

Sahabbai 12 da aka fi ruwaito hadisan Annabi S.A.W. daga garesu

Tarihin Sahabbai Mata 3: Ummu Adiyya Al-Ansariyya